Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta ce, ta daƙile gobarar da ta tashi yau Juma’a a babban titin Abeokuta zuwa jihar.
Daraktar hukumar, uwar gida Margaret Adeseye, ce ta bayyana haka yayin da take yin ƙarin haske kan lamarin tana mai cewa mutum ɗaya ya mutu a gobarar, yayin da motoci uku da wasu shaguna kuma suka ƙone sanadiyyar malalar man fetur.
Haka kuma ta ce, malalar man ta afku ne daga wata tankar mai a unguwar Ajegunle, kusa da tashar motocin bas.
Sanarwar ta ce, “Rahotannin lamarin sun isa hukumar ne da misalin ƙarfe 2:16 na wayewar garin yau Juma’a.”
“Hatsarin ya faru ne a lokacin da wata tanka mai ɗauke da lita 45,000 na na fetur ke shirin juyawa a kan babbar hanyar a kan hanyarta ta zuwa wani gidan mai.”
“Malalar ta bazu zuwa bakin titi kuma inda bayan mazauna yankin sun fara leƙowa don ganin abinda ke faruwa nan take wuta ta tashi.”
“Mutane biyun sun yi sakaci da rayukansu, don haka wannan ma’aikata na gargaɗin mazauna garin da kada su riƙa ɗibar mai idan yana zuba.” in ji sanarwar.
Adeseye ta ce, har yanzu jami’an bayar da agajin gaggawa na wurin domin tabbatar da cewa an kawar da duk wani cikas na zirga-zirga.
Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa an shawo kan lamarin saboda ana ci gaba da aikin kwashe gawawwaki da kuma sauran kayan da gobarar ta ɓarnatar.”










































