Daga Muazu Muazu-Kano
Allah Ya sake zagayo da mu wata shekara, kuma cikin wata na Tara a kalandar Musulunci addinin gaskiya, wanda Manzon Allah (S.A.W) ya zo da shi don ya zama hanyar tsira ga wadanda suka bi shi.
Watan Ramadan shi ne watan da Allah ya saukar da Alqur’ani mai girma, shi ne watan kasafi ga bayin Allah, kuma watan ibada, watan gafara da rahama, watan da a cikin sa Allah ya ke yin kasafi duk abin da zai faru a shekara, yayin da Zai umarci mala’kunsa su rubuta.
Tafiya ta yi nisa sosai a cikin azumin wannan shekara, domin ga shi har mun shigo goman karshe a cikin kwanakin wannan wata mai alfarma da daraja.
Kwanakin da suka kasance tamkar gwalagwale a cikin duhun dare, domin a cikin su ne ake rubanya ibada ga Allah (S.W.T), shi ma sai ya rubanya ladan ibadar ninkin ba ninkin ga wanda ya aikata ta.
Idan mutum ya yi sadaka a cikin wadannan kwanaki to ladan ta ba dai dai yake da na sauran kwanaki ba ko wasu watanni da suka wuce a baya.
Duk wani aikin ibada da mutum ya gabatar, kamar Sallah ko zakkah da zikiri da dai sauransu, Allah yana rubanya ladan.
Kuma a cikin wadannan kwanaki ne Allah Ya saukar da wani dare mafi daraja daga cikin darare.
Daren da darajar sa tafi ta watanni dubu, wato fiye da shekara tamanin kenan (80yrs).
Wannan dare shi Allah Ya kira da LAILATUL QADR, wato daren kaddara, daren da Allah Ya ke mika wa mala’iku kundin aikin su na wata shekara domin aiwatar wa, kwatankwacin yadda shugabannin mu suke yi wajen kasafin kudi a wannan duniya.
A cikin wannan dare ne mala’iku ke sauka a saman duniya domin amsa bukatar bayin Allah masu ibada a cikin wannan dare, su dauke ta zuwa ga Allah.
A cikin wannan dare ne Allah ta ke yin gafara ga miliyoyin bayin Sa.
Kazalika a cikin sa Allah yake amsa duk wata bukatar bayinsa.
A cikin sa Ya ke rahama da gafara, kuma a cikin sa ne ya ke rabon aljanna, kuma a cikin sa ne Ya ke rabon arziki, a cikin sa ne ni’ima take sauka ta lullube duniya tun daga yammaci har zuwa wayewar gari.
Allah mai girma da daukaka a cikin wannan dare ya ke hana duk wata halitta da ba Dan Adam ba cutar da Dan-Adam ta hanyoyi da dama, ko Dan Adam din ne ba a ba shi ikon cutar da dan uwansa, saboda rahamaniyya irin ta Ubangijin talikai.
A karshe ina yi mana addu’ar Allah Ya ba mu ikon dagewa da ibada a gareshi, a cikin RAMADAN da bayan ramadan, ya Allah ka ba mu kwarin gwiwar ci gaba da ayyukan ibada a cikin wannan wata, ina kuma rokon Allah ya ba mu ladan azumi cikakke, ya sa mu dace mu rabauta da wannan dare na LAILATUL QADR, ya sanya mu cikin bayin Sa da zai ‘yantar a cikin wannan wata. Ameen summa Ameen.