Wani dan Najeriya mai wankin mota ya fada cikin matsala bayan ya tuka motar da aka kawo masa wanki zuwa wajen siyan teba da miya sannan ya yi kaca-kaca da motar.
A cikin bidiyon da @drive234 ya wallafa a TikTok, an ga mai wankin motar yana duke kan gwiwowinsa tare da rokon mai motar da ya gafarta masa.
Motar ta lalace sosai kuma saurayin ya yi nadama amma bidiyon bai nuno ko an yafe masa ba.














































