Hukumar jindadin alhazai ta jihar Kano ta sanar da mutuwar wasu maniyyata biyu a wani hadarin mota da ya ritsa da su a kan hanyar Rimin Gado a jihar Kano.
A wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Sulaiman A. Dederi ya sanyawa hannu, ya tabbatar da rasuwar mutanan.
Mamatan sun hada da, Alkasim Ibrahim Walawa, mai shekara 48 da mahaifiyarsa Hadiza Garba mai shekara 73, wadanda ke kan hanyarsu domin fara shirye-shiryen tafiya kasa mai tsarki, a lokacin da mummunan hatsarin ya auku.
Alkasim, ya rasu ya bar mata biyu da yara bakwai, yayin ita kuma mahaifiyar shi, Hadiza Garba ta bar ‘yaya biyar. Mamatan biyu, sun kasance ‘yan asalin kauyen Walawa ne a karamar hukumar Kabo da ke jihar Kano.
Hukumar ta bayyana kaduwarta da mutuwar maniyyatan, inda ta bayyana cewa mutanan suna kan hanyarsu ne domin gabatar da ibada lokacin da hadarin ya ritsa da su.
Jaridar SolaceBase, ta rawaito cewa hukumar ta aike da sakon ta’aziyya a madadin hukumar da ma’aikatanta, ta kuma roki Allah ya gafarta wa mamatan.
“Muna addu’ar Allah ya gafarta musu zunubansu, ya kuma sa Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare su.” In ji sanarwar.
Hukumar ta kuma aike da sakon ta’aziyya ga iyalan mamatan, inda ta bukace su da su yi hakuri a wannan mayuyacin halin.












































