Kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ta bayyana cewa “babu gudu ba ja da baya” game da gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi na kwanaki biyu daga ranar 27 zuwa 28 na wannan wata da muke ciki na Febrairu a fadin kasar.
Shugaban kungiyar Comrade Joe Ajero ne ya bayyana hakan a matsayin martani ga gargadin da hukumar tsaron ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta yi musu kan gudanar da zanga-zangar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito.
Karin labari: Libya: ƙungiyoyi masu makamai za su fice daga birnin Tripoli
Tun da farko, hukumar tsaron ta ‘yan sandan sirri, ta gargadi shugabancin kungiyar kwadagon da takwaransa na TUC kan cewa su janye zanga-zangar da suke shirin yi domin barazana ce ga tsaron kasar.
Sai dai a martaninsa ga hukumar, Shugaban NLC Ajero, ya ce “tarihi ba zai yafewa kungiyoyin kwadagon ba, idan har suka zuba ido halin matsin rayuwa da al’umma ke ciki ya ci gaba da tafiya” in ji shi.
Ya cigaba da cewa, “wannan ya faru ne sakamakon abin da ake kira da mulkin rashin tausayi na gwamnatin Najeriya da mukarrabanta” in ji Ajero.