Libya: ƙungiyoyi masu makamai za su fice daga birnin Tripoli

libya, Tripoli, kungiyoyi,
Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke riƙe da birnin Tripoli sama da shekaru goma sun amince su bar babban birnin ƙasar Libya...

Ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai da ke riƙe da birnin Tripoli sama da shekaru goma sun amince su bar babban birnin ƙasar Libya.

Ministan harkokin cikin gida Imad Trabelsi ya ce bayan tattaunawa mai tsawo an cimma yarjejeniyar cewa ‘ƴan sanda gwamnati su ne za su dinga tabbatar da tsaro.

Ya shaidawa manema labarai cewa za’a samu ‘yan sandan gaggawa da jami’an birnin da kuma masu binciken laifuka kadai daga wurinsu.

Karin labari: Nijar ta karɓi baƙuncin tawagar Iran

Matakin ya biyo bayan kazamin faɗan da aka yi a baya-bayan nan.

Ƙasar Libya dai ta fuskanci ƙalubalen tsaro tun bayan hamɓarar da gwamnatin Muammar Gaddafi a shekara ta 2011, inda ƙasar ta rabu tsakanin gwamnatin yammacin ƙasar karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibah da kuma gwamnatin gabashin ƙasar karkashin jagorancin Khalifa Haftar.

Ya ce da zarar ƙungiyoyin sun fice daga babban birnin ƙasar wasu biranen za su bi baya, yana mai cewa “ba za’a sake samun shingayen binciken ababen hawa ba, da kuma sauran kungiyoyi masu dauke da makamai a kan tituna ba”

Karin labari: Akpabio ya fallasa gwamnoni da karbar Naira Biliyan 30

Yarjejeniyar za ta sa akalla kungiyoyi biyar ɗauke da makamai su bar birnin Tripoli a karshen watan Ramadan a ranar 9 ga watan Afrilu, ciki har da wanda ke da sansani a yankin da aka kashe mutane 10 a karshen mako.

Ƙungiyoyin masu ɗauke da makamai da ake magana a kai sun haɗa da rundunar tsaro da rundunar tsaro ta musamman da Birgediya 444 da Brigade 111 da kuma Hukumar Tallafawa Zaman Lafiya, suna da muggan makamai tare da raba yankuna da dama a tsakaninsu.

Karin labari: Kamfanonin siminti sun amince rage farashin siminti

Sai dai sau da yawa sun kasance suna fafatawa da junansu, ciki har da wani lamari da ya faru a watan Agusta wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 55 tare da jikkata kusan 150.

Ba sa ƙarƙashin ikon gwamnatin Libya kai tsaye, amma suna samun tallafin jama’a. An ba su ‘yancin gudanar da ayyukansu ne ta hanyar matsayi na musamman da gwamnati ta ba su a cikin 2021.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here