Kamfanonin siminti sun amince rage farashin siminti

kamfanoni, siminti, rage, farashi,
Kamfanonin siminti da ke Najeriya sun amince su rage farashinsa tsakanin naira dubu 7 da dubu 8 akan buhu mai nauyin kilogiram 50, ya danganta da nisan wurin...

Kamfanonin siminti da ke Najeriya sun amince su rage farashinsa tsakanin naira dubu 7 da dubu 8 akan buhu mai nauyin kilogiram 50, ya danganta da nisan wurin a fadin kasar.

Kamfanonin da suka halarci ganawar sun kuma bayyana aniyar rage farashin siminti da zarar gwamnati ta cika alkawuran da ta daukar musu.

An cimma wannan yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayyar da kamfanonin simintin a yayin wata ganawa da Ministan Ayyuka Sanata David Umahi ya shirya a Abuja.

Karin labari: Zaɓen fitar da gwanin gwamnan Edo bai kammala ba – APC

A cewar sanarwar da ma’aikatar ayyukan ta fitar, kamfanonin sarrafa simintin da gwamnatin tarayya sun amince cewar farashin simintin yayi bambarakwai a wasu sassa na Najeriya. A zahiri bai kamata farashin buhun siminti me nauyin kilo 50 ya zarta tsakanin naira dubu 7 da dubu 8 ba.

“Don haka, kamfanonin simintin uku da suka hada da Dangote da BUA da kuma Lafarge suka amince cewar farashin buhun siminti me nauyin kilo 50 ba zai zarta tsakanin naira dubu 7 da dubu 8 ba ya danganta da nisan wuri.”

Karin labari: MDD ta ware dala miliyan 100 don ayyukan jinkai a kasashe 7

“Gwamnatin ta kuma shawarci kamfanonin sarrafa simintin dasu fitar da tsarin da zai rika daidaita farashi tare da tabbatar da yin biyaya ga shi a nan gaba, sa’annan kamfanonin sun amince da shawarar aiwatar da hakan tare da hukunta dilolinsu da aka samu karya ka’idar.”

Sanarwar ta ci gaba da cewar, “gwamnatin na sa ran farashin simintin ya sauka bayan cika alkawuran da ta dauka na magance matsalolin kamfanonin akan iskar gas da harajin shigo da kaya da simogal din kaya da kuma gyaran hanyoyi. An amince a sake taruwa nan da kwanaki 30 domin nazarin irin ci gaban da aka samu.”

A cewar Uzoka Anite, ana ci gaba da kokari wajen magance dalilan da suka sabbaba hauhawar farashin kayan masarufi lokaci guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here