MDD ta ware dala miliyan 100 don ayyukan jinkai a kasashe 7

MDD, kasashe, naira, miliyan, ayyukan jinkai
Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta ware dala miliyan 100 domin gudanar da ayyukan jin kai a kasashe bakwai da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar...

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa ta ware dala miliyan 100 domin gudanar da ayyukan jin kai a kasashe bakwai da suka hada da Jamhuriyar Demokradiyyar Kongo da Sudan da kuma Syria.

Tallafin, wanda Asusun bada Agajin Gaggawa na Majalisar Dinkin Duniya, ya samar a wannan lokaci shi ne mafi kankanta a cikin ‘yan shekarun nan, yayin da kungiyoyin agaji ke kokarin janyo hankulan takwarorinsu wajen bayar da tallafin jinkai a yankunan da ake yin rikice-rikice.

Karanta wannan: Gwamnatin Sokoto ta haramta fitar da kayan abinci zuwa wasu garuruwa

A wata sanarwa da ofishin da ke kula da ayyukan jin kai na majalisar ya fitar ya nuna yadda kudaden da asusun ke samarwa ya ragu a shekarar 2023, wanda shi ne mafi karanci tun daga 2018.

A shekarar 2023 dai tsananin bukatun agaji a duniya suka kai kusan dalar Amurka biliyan 57, yayin da tashe-tashen hankula da suka mamaye sassa daban-daban na duniya da suka hadar da yakin Isra’ila da Hamas da sauran su.

Karanta wannan: MDD ta ƙaƙaba takunkumi kan jagororin ‘ƴan tawayen Kongo

Sanarwar ta ce a watan da ya gabata kadai an samu gazawar kudaden da za’a gudanar da ayyukan jin kai da kusan dalar Amurka biliyan 35.

Baya ga kasashen Congo da Sudan da Syria, za kuma ayi amfani da kudaden agajin da aka ware wajen daukar matakan magance rikicin kasashen Chadi da Nijar da Lebanon da kuma Honduras.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here