Kotu ta bada umarnin yiwa Murja gwajin kwakwalwa 

download

A yau kotun shari’ar Muslunci ta Gama PRP ta yanke hukunci kan shari’ar shahararriyar ‘yar TikTok Murja Ibrahim Kunya. Mai shari’a Nura Yusuf Ahmad ya nemi da a kai Murja zuwa asibiti don duba lafiyar kwakwalwarta.

Sai dai, tun lokacin da aka ce hukumar Hisbah ta Kano ta kama Murja, mutane ke ci gaba da tofa albarkacin bakin su, musamman yadda ta yi kaurin suna a TikTok.

Maganganun jama’a sun kara yawaita bayan da aka samu rahoton cewa an fitar da Murja daga gidan gyara hali da aka kaita ajiya na wani lokaci.

Solacebase ta tattara wasu abubuwa biyar da ya kamata ku sani game da shari’ar Murja Ibrahim Kunya.

1. Murja ba ta amsa laifin da ake zargin ta aikata ba Bayan da hukumar Hisbah ta Kano ta gurfanar da Murja a gaban kotu, aka kuma karanta mata laifukan da ake tuhumarta da su, ta karyata aikata su. An tuhumi Murja da yada bidiyon badala, bata tarbiyyar jama’a kamar yadda wasu mazauna unguwar da take suka kai koke ga Hisbah.

Bayan kin amsa laifin, mai shari’ar ya tura ta zuwa gidan gyaran hali har zuwa ranar 20 ga watan Fabrairu (yau) don ci gaba da shari’ar.

2. An fitar da Murja daga gidan gyaran hali, an samu sabani Da farko, mai magana da yawun kotun ya ce ba su da masaniyar an saki Murja daga gidan yarin, saboda umarnin ajiyarta alkali ya bayar.

Amma da maganar ta fara yaɗuwa a cikin jama’a, kakakin gidan gyaran hali na jihar Kano, Misbahu Lawal Kofar Nassarawa ya ce kotun da ta tura Murja gidan ce ta ce a fitar da ita.

Ado Fage ya kuma yin amai ya lashe, inda ya fitar da sanarwar cewa an fitar da Murja ne don gudanar da sabon bincike bisa yarjewar alkali.

3. Gwamnati na goyon bayan Murja, cewar mutanen Kano Mutanen Kano da suka yi tsokaci kan zargin an saki Murja daga gidan yarin, sun ce akwai alamar sa hannun gwamnatin jihar a ciki.

4. Har yanzu Daurawa ne shugaban Hisbah na Kano Akwai rade-radin da aka yi yadawa na cewar Mallam Aminu Daurawa ya yi murabus daga shugaban Hisbah saboda an saki Murja.

wata majiya a hukumar, an tabbatar da cewa Daurawa bai yi murabus ba, kuma ya shiga ofis ranar Litinin. Daga bisani ne mataimakin kwamandan hukumar, Mujahid Aminundeen ya fitar da sanarwar ƙaryata jita-jitar. 5. Gwamnatin Kano ba za ta tsoma baki a shari’ar Murja ba

A yammacin ranar Litinin, kwamishinan watsa labarai na jihar Kano, Baba Halilu Dantiye ya fitar da sanarwar cewa babu ruwan gwamnati a fitar da Murja daga gidan gyaran hali. Dantiye ya kuma jaddada cewa gwamnatin jihar ba za ta tsoma baki a shari’ar Murja ba, sabanin yadda wasu ke zargin ta da hannu a sakinta. Kotu ta ba da umarni a yi wa Murja gwajin ƙwaƙwalwa A safiyar yau Talata, Legit Hausa ta ruwaito cewa kotun shari’ar Muslunci da ke da zama Gama PRP a jihar Kano, ta ce za a gudanar da gwajin ƙwaƙwalwa ga Murja Kunya don sanin abin da ke damunta.

Alkalin kotun, Nura Yusuf Ahmad, ya ce take-taken Murja sun nuna akwai aljanu a jikinta ko kuma aikin kayan maye ne kawai. Ahmad ya ce Murja za ta zauna karkashin kulawar likitocin ƙwaƙwalwa da hukumar Hisbah na tsawon watanni uku.

Legit Hausa

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here