
Tarin mata da kananan yara na ci gaba da bin dogayen layuka don karbar tallafin abinci a manyan dakunan girkin da aka samar a arewacin Gaza bayan da kasashe suka fara amfani da salon jefa agajin abincin ta sama ta hanyar amfani da jirage.
Rahotanni sun bayyana cewa kasashen Jordan da Masar da kuma Amurka su ke kan gaba wajen amfani da salon na jefa agajin abincin ta sama a yankin Gaza.
Karin labari: ‘Yan bindiga sun sace dalibai da malaman makaranta 200 a Kaduna
Matakin kasashen na da nufin samar da sauki ga matsananciyar yunwar da al’ummar ta Gaza ke fuskanta sakamakon yadda Isra’ila ta dakile duk wasu hanyoyin shigar da agajin abinci yankin.
Bayanai na nuni da cewa zuwa yanzu akwai fararen hular da yawansu ya kai dubu 300 da ke rayuwa a arewacin Gaza duk da umarnin Isra’ila na ganin babu sauran ko mutum guda da ya rage a yankin tun bayan fara luguden wutar sojinta a watan Oktoban bara.
Karin labari: “Herbert Wigwe ya taimake ni bayan sauke ni daga sarkin Kano” – Sanusi II
A cewar rahotanni al’ummar da ke rayuwa a yankin na Arewacin Gaza basa iya samun tallafin komai sakamakon yadda aka katsesu daga sauran sassan yankin na Falasdinu lamarin da ya ta’azzara yunwar da al’umma ke fama da ita.
A ranara 20 ga watan Fabarairun da ya gabata ne shirin abinci na Majalisar Dinkin Duniya WFP ya sanar da dakatar da shigar da agajin abinci Gaza sakamakon yadda Isra’ila ta farmaki tawagar motocin jami’an hukumar.












































