Majalisar Senegal ta amince da shirin Sall na afuwa ga ‘yan adawa

Majalisar, Senegal, Macky Sall, afuwa, fursunoni
‘Yan majalisar Senegal sun amince da kudirin afuwa ga fursunonin siyasar kasar wanda shugaba Macky Sall ya gabatar gabansu duk kuwa da tarnakin da ke tattare...

‘Yan majalisar Senegal sun amince da kudirin afuwa ga fursunonin siyasar kasar wanda shugaba Macky Sall ya gabatar gabansu duk kuwa da tarnakin da ke tattare da kudirin wanda ya haddasa rarrabuwar kai a zauren Majalisar dokokin kasar.

Bayan tafka doguwar muhawara ne a ranakun Talata da Laraba ‘yan majalisun 94 suka goyi bayan kudirin yayin da 49 suka kalubalance shi.

Karin labari: Kasashe sun fara amfani da jirage wajen jefa agajin abinci a Gaza

Kafin wannan muhawara dai tun a ranar Talata Majalisar ta yi watsi da kudirin wanda ta ce ba shi ne mafita ga halin da Senegal ke ciki ba.

Shugaba Macky Sall na son amfani da shirin afuwar don kwantar da hankula a rikicin siyasar da Senegal ta fada wanda zai kai ga sakin tarin fursunonin siyasar da ke tsare.

Karin labari: ‘Yan sanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa a Najeriya

Haka zalika shirin afuwar zai kuma bayar da damar sakin hatta dubunnan magoya bayan madugun adawa Ousmane Sonko wadanda suka rika jagorantar mabanbantar bore tun faro dambarwar dan adawar da shugaba Sall.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here