Ana tuhumar mahaifiyar yarinyar nan mai shekaru 6 da ta ɓata a Afirka ta Kudu da laifi fatauci da garkuwa da diyarta.
An gabatar da wannan tuhuma ne a kan Kelly Smith tare da saurayinta da wasu mutane biyu a shari’ar da ta ba da mamaki a kasar.
Joslin Smith ta ɓata a wajen gidansu da ke kusa da birnin Cape Town a ranar 19 ga watan Fabarairu.
Karin labari: Majalisar Senegal ta amince da shirin Sall na afuwa ga ‘yan adawa
Bincike ya gano rigarta da jini a jiki, amma ba’a ga yarinyar ba, duk da binciken da aka ƙaddamar na hadin-gwiwa da sojojin sama da jirage marasa matuka da karnuka.
Kafin wannan lokaci mahaifiyar yarinyar ta ce ba za ta saduda ba har sai an gano diyarta ta a raye.
A cikin kowanne sa’a biyar ana samun rahotannin ɓatan yara a Afirka ta Kudu.