Tsofaffin daliban cibiyar nazarin siyasa da dabarun mulki ta Kasa zasu gudanar da taron hadin kan Kasa

AANI 2
AANI 2

Kungiyar tsofaffin daliban Cibiyar Nazarin Siyasa da Dabarun mulki ta kasa (AANI), ta shirya gudanar da wani babban taro domin tattaunawa kan hadin kan kasa.

Sakataren yada labaran Kungiyar ta Kasa, AANI, Birgediya Janar Sani Kukasheka Usman, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba a Abuja.

Usman ya ce kungiyar ta damu da abubuwan da ke kawo raba kan kasar nan, don haka akwai bukatar a gudanar da taron.

Ya ce taron mai taken, “Hadin kan Yan Najeriya wajen gudanar da babban zaben 2023”, zai gudana a ranar 20 ga watan Satumba.

Usman ya ce tun lokacin da aka kafa cibiyar a shekarar 1979 ta ci gaba da zama wata kafa ta nazari akan manufofin jama’a a Najeriya.

“A matsayinmu na wasu daga cikin masu ruwa da tsaki a Najeriya, mun damu matuka game da yadda kasar nan ke kara fuskantar tabarbarewar rashin tsaro da ta’addanci, tare da rikicin kabilanci, musamman a lokacin da ake tunkarar babban zabe na 2023.

Mai magana da yawun Kungiyar ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci taron yayin da Janar Martin-Luther Agwai mai ritaya zai kasance babban jigo.

Agwai ya kasance tsohon babban hafsan hafsoshin tsaro kuma tsohon mai ba da shawara na musamman ga babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya kan harkokin wanzar da zaman lafiya.

Har ila yau, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad-Abubakar na 3, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar AANI Heritage Council, shi ne zai kasance uban taro na wannan rana, yayin da ministan babban birnin tarayya, Malam Mohammed Bello, zai kasance babban mai masaukin baki.

Sauran fitattun ‘yan Najeriya da ake sa ran za su halarci taron sun hada da, Gwamna Babagana Zullum na Borno da gwamnan Jigawa Badaru Abubakar da sauran gwamnonin kasar nan.

Sauran sun hada da ‘yan majalisar tarayya da ministoci, da kuma fitattun ‘yan Najeriya daga sassa daban-daban da dai sauransu,” inji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here