Gwamna Babagana Umara Zulum ya amince da nadin Baba Bura Usman a matsayin sabon Akanta Janar na jihar Borno.
Mai magana da yawun Gwamnan, Malam Isa Gusau, ne ya sanar da nadin a wata sanarwa da ya fitar a daren Laraba.
Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa Baba Bura Usman, a baya ya kasance daraktan ayyuka na baitulmali a ma’aikatar kudi, kasafin da tsare-tsare ta jihar Borno, daga shekarar 2020 har zuwa lokacin da aka nada shi.
Sanarwar ta ce, Usman mai shekara 57, wanda ya fito daga karamar hukumar Kaga ta arewacin jihar Borno, gogaggen Ma’aikaci ne wanda ya shafe sama da shekaru 20 a fannin hada-hadar kudi da tsarin kula da harkokin cikin gida, in ji sanarwar.
Ya kara da cewa, akanta Janar din tun 1990, ya kasance yana aiki a matsayin mataimakin Akanta a wani kamfani mai zaman kansa, Premier Property Dev Co. Ltd, kafin ya koma aikin Gwamnatin jihar Borno a matsayin babban Akanta wanda aka tura shi cibiyar fasaha da raya al’adu ta jihar Borno dake Maiduguri, babban birnin Jihar a shekarar 1998.
Usman ya kasance Babban Akanta (Mai fitar da kudi) a gidan gwamnati da ke Maiduguri a shekarar 2001 kuma ya kasance Babban Akanta a Sashen Kasafin Kudi da Tsare-tsare a shekarar 2003, a hukumar Ilimin bai daya ta Jihar Borno a 2010 da kuma Ofishin Fansho na Jihar Borno, a shekarar 2017 kafin daga bisani a shekarar ya zama daraktan fansho na jihar Borno. Inji Sanarwar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa a shekarar 2018, Usman ya zama shugaban sashin kula da harkokin kudi na jihar (PFMU).
Usman ya kuma yi aiki a hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Borno (RUWASSA) kafin ya zama daraktan ayyuka na baitulmali a shekarar 2020 har zuwa nadinsa a yanzu.
Sanarwar ta kara da cewa sabon Akanta Janar din ya yi karatun Digiri na farko a fannin Accountancy, ya yi Post-Graduate Diploma a fannin Kudi da Kuma Digiri na biyu a fannin kimiyyar kare aukuwar hadari da bala’o’i duka daga Jami’ar Maiduguri.
Ya kuma yi karatun Diploma (ND) da babbar Diploma (HND) a fannin harkokin kasuwanci duk a kwalejin kimiyya ta Ramat dake Maiduguri.
Usman ya halarci kwasa-kwasan kula da hada-hadar kudi a Najeriya da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, kuma ya samu takardun shaida a Advanced Financial Management, Information Technology da kuma International Public Sector Accounting Standards (IPSAS) da kuma kwarewa a fannin kwamfuta, in ji Gusau.
Sabon Akanta Janar din dai dan kungiyar Akantoci ne ta kasa (ANAN), kana Usman kuma memba ne a Majalisar bada rahoto kan harkokin Kudi ta Najeriya, da kuma Cibiyar bada horo kan tattara Haraji ta Najeriya.
Sabon Akanta Janar din ya karbi ragamar mulki daga hannun Mai Adamu Ya’u wanda ya yi ritaya a baya-bayan nan.













































