Kotun kolin kasar nan ta bayyana Ifeanyi Chukwuma Odii, a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar Ebonyi na Shekarar 2023.
Da yake yanke hukunci mai shari’a Lawal Garba, ya ce Sanata Joseph Obinna Ogba, mai wakiltar mazabar Ebonyi ta tsakiya, ba shi da hurumin shigar da kara a kotun.
Ya ce kotun daukaka kara da ke Abuja ba ta da hurumin karbar kara a matakin farko tun da dai Ogba ba ya cikin jam’iyya a dukkan shari’ar da kotun ta gudanar (wata babbar kotun tarayya da ke zaune a Abakaliki).
Alkalin kotun ya ce gaba dayan shari’ar da kotun daukaka karar ta gudanar bata da hurumi a ciki.
Don haka Garba ya yi watsi da hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke a ranar 19 ga watan Yuni, inda ta bayyana Ogba a matsayin dan takarar jam’iyyar da ya dace.
Ya kuma ce karar da Ogba, wanda ake kara na 1, ya shigar a gaban kotun daukaka kara, an yi ta ne ba tare da bin doka ba.
Mai shari’a Amina Augie da sauran alkalai a kwamitin sun goyi bayan hukuncin na Garba, inda suka bayyana hukuncin a matsayin wanda ya dace.
Kamfanin dillancin labarai na Kasa (NAN) ya ruwaito cewa Mista Odii da Sanata Ogba sun yi takun-saka kan wanda aka zaba a matsayin dan takarar jam’iyyar a zaben 2023 a zaben fidda gwani na jam’iyyar da ya gudana a lokuta mabanbanta a jihar.
Kamfanin dillancin Labaran ya Kara da cewa kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja, a kwanakin baya, ta bayyana Ogba a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar a jihar, yayin da ta yi watsi da hukuncin kotun da ke zamanta a Abakaliki da ta bayyana Odii a matsayin dan takarar PDP.
Amma Odii, bai gamsu da hukuncin kotun ba, Inda ya shigar da wata karar mai lamba: SC/CV/ 939/2022 a kotun koli. A karar, Odii ya kai karar Ogba da Jam’iyyar PDP da Kuma hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).













































