Shugaban hukumar kula da ‘yan sanda ta kasa Musiliu Smith ya ajiye mukaminsa.
Mai magana da yawun Hukumar, Ikechukwu Ani, shi ne ya tabbatar da murabus din ga manema labarai a ranar Laraba.
Ani ya bayyana cewa Smith ya yi murabus ne bisa dalilai dake da jibi da lafiya, kuma matakin ya samu karbuwa daga shugaban kasa Muhammadu Buhari.
“Ya yi murabus da kan sa bisa dalilan lafiya kuma shugaban Kasa ya amince da murabus din,” in ji Ani.
Ani ya Kara da cewa har yanzu hukumar ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan murabus din Smith ba.
Amma dai rahotanni sun ce Smith wanda ke zama tsohon sufeta janar na ‘yan sandan kasa, ana sa ran zai mika ragamar aiki ga Justice Clara Ogunbiyi mai ritaya.













































