Kotun hukunta manyan laifuka a kasar Birtaniya ta dage shari’ar da ake yi wa Sanata Ike Ekweremadu da matar sa.
Ekweremadu da matarsa, Béatrice na fuskantar tuhuma kan hada baki wajen safarar sassan jikin Dan Adam.
Sai dai kuma, ana zargin wani mutum na uku Mai suna Obinna Obeta, wanda ke aikin likita a Landan.
Kotun hukunta manyan laifuka ta kasar ta ce ana sa ran kammala shari’ar a shekarar 2023.
An Sanya ranar 31 ga watan Oktoba Mai zuwa a matsayin ranar da za a fara shari’ar da tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, da matarsa, da Obeta.
Idan dai za a iya tunawa, an hana dan majalisar da matar sa beli tare da tsare shi a gidan yari yayin da aka dage shari’ar zuwa ranar 7 ga watan Yuli da kuma ranar 4 ga watan Agustan 2022.
Sai dai a wani yanayi na daban, an bayar da belin Beatrice, matar Ekweremadu bisa wasu tsauraran sharudda, biyo bayan bukatar da lauyan wadanda ake tuhuma ya shigar.
An bayar da belin ne a ranar 22 ga Yuli, 2022.

Sai dai kuma kotun ta ki amincewa da bukatar belin Ekweremadu makamancin haka.













































