An nada Sanata Dino Melaye da Daniel Bwala a matsayin masu magana da yawun dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP kuma tsohon mataimakin shugaban kasar nan, Atiku Abubakar, a yakin neman zaben shugaban kasa mai zuwa.
Bayanin hakan na zuwa ne a cikin wata sanarwa da mai baiwa Atiku shawara kan harkokin yada labarai Paul Ibe ya sanyawa hannu a ranar Alhamis.
Sanarwar ta ce nadin na biyu ya fara aiki nan take.

Dino Melaye dai ya kasance dan siyasa kuma dan majalisar dattawa zubi na 8, wanda ya wakilci Kogi ta Yamma, ya kuma fito daga Ayetoro Gbede da ke karamar hukumar Ijumu a jihar Kogi.
Yayin da shi Kuma Bwala, a daya bangaren, kwararre ne a fannin shari’a, dan siyasa kuma manazarci harkokin jama’a, ya fito daga jihar Adamawa.













































