PDP: Ɗan takarar gwamna a Bauchi ya janye wa Bala Mohammed

images10
images10

Ɗan takarar gwamna a jihar Bauchi karkashin jam’iyyar PDP, Ibrahim Kashim, ya janye wa gwamna Bala Muhammad takararsa.

DAILY NIGERIAN ta ruwaito cewa Kashim ya bar wa gwamnan takarar ne, bayan da Bala Muhammad ya sha kaye a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa da jam’iyyar PDP ta gudanar.

Mai magana da yawun jam’iyyar a jihar ta Bauchi Yayanuwa Zainabari, ne ya shaida wa manema labarai hakan jiya Talata yana mai cewa Kashim ya janye daga takarar ne bisa ra’ayin  kansa.

Ya ƙara da cewa  jam’iyyar  za ta bi tsarin da ya dace domin maye gurbin Kashim da wani ɗan takarar.

“Za mu bayyana matsayar mu a cikin wannan makon.

“Abinda kaɗai ya rage wa jam’iyyarmu shi ne ta bai wa INEC sunan wanda zai maye gurbinsa domin cika ƙa’idoji ,” in ji shi

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here