Ƙungiyar cigaban Masarautar Birnin Gwari BEPU ta koka kan yadda wasu ƴan ta’adda suka yi garkuwa da dimbin matafiya da daliban da suka rubuta jarrabawar makarantar kiwon lafiya ta jami’ar Jihar Kaduna da sanyin safiyar yau Talata.
Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar Idris Sa’idu ya fitar, ta sanar da hakan yau Talata a Kaduna, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.
A cewar sanarwar, ƴan fashin sun yi wa wasu wurare uku ƙawanya a kan babbar hanyar inda suka tilasta wa masu ababen hawa yin cirko-cirko.
Wadanda tsautsayin ya ritsa da su sun faɗa tarkon da ƴan fashin suka ɗana, daga bisani suka yi awon gaba da su.
Sanarwar ta ce, an sace matafiya da dama da ɗaliban da za su rubuta jarabawar shiga makarantar aikin lafiya.
“Bai kamata a ɗauki wannan lamari da wasa ba saboda tsaron rayuka da dukiyoyin mutanenmu.”
Sanarwar ta bayyana cewa, ta hannun Malam Mu’azu Idris, hukumar makarantar ta amince da dage jarrabawar.
Sai dai har yanzu rundunar ƴan sandan Kaduna da gwamnatin jihar ba su ce komai ba dangane da faruwar lamarin.













































