Mjalisar dokokin jihar Kaduna, ta dakatar da shugaban ƙaramar hukumar Chikun Salisu Musa, da takwaransa na ƙaramar hukumar Giwa Abubakar Lawal, bisa zargin karkatar da kuɗaɗe.
Ƴan majalisar sun ɗauki matakin ne a zaman majalisar na yau Talata biyo bayan ƙudurin da dan majalisar mai wakiltar mazabar Zaria Kewaye, Alhaji Ahmed Chokali ya gabatar.
A cewarsa, majalisar ba za ta iya ci gaba da zuba ido ba yayin da shugabannin ƙananan hukumomin ke ci gaba da yin watsi da ƙa’idojin gudanar da ƙananan hukumomin jihar.
Chokali ya gabatar da bukatar cewa majalisar ta gudanar da bincike kan lamarin.
“Na tsaya nan ne domin in gabatar da ƙudirin cewa majalisa ta gudanar da bincike a karkashin sashe na 128 na kundin tsarin mulkin Najeriya domin a binciki al’amuran ƙananan hukumomin biyu,” inji shi.
Ya kuma buƙaci majalisar da ta dakatar da shugabannin biyu domin gudanar da bincike mai inganci.
Ya ce shugabannin su miƙa al’amuran ƙananan hukumomin ga mataimakan su.
Zaman majalisar wanda shugabanta Alhaji Yusuf Zailani ya jagoranta, daga bisani ya dakatar da shugabannin biyu.
Majalisar ta umurci kwamitin majalisar kan harkokin ƙananan hukumomi da ya gudanar da bincike tare da bayar da rahoto daga baya.












































