Hatsarin mota ya yi sanadiyar mutuwar mutum 12 da jikkatar mutum 28

Hatsarin mota, mutuwar, zaria, kano
Hatsarin mota da wata mota kirar kirar KTG 454 ZZ ya afku a kan hanyar Zaria zuwa Kano wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu 28...

Hatsarin mota da wata mota kirar kirar KTG 454 ZZ ya afku a kan hanyar Zaria zuwa Kano wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12 tare da jikkata wasu 28.

SOLACEBASE ta rawaito cewa hatsarin da ya afku a kauyen tashar Yari da misalin karfe bakwai da rabi na safiyar ranar Litinin, kamar yadda hukumar kiyaye hadurra ta kasa FRSC ta bayyana hakan na da nasaba ne da gudun wuce gona da iri.

Wata sanarwa da ofishin yada labarai na hukumar FRSC da ke Kaduna ya fitar a ranar Litinin, ta ce shugaban karamar hukumar Makarfi da kwamandan runduna tashar Yari sun isa wurin domin tantance lamarin.

Karin labari: Za mu tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abinci – NEMA

“Bugu da kari, bincike kan lamarin ya nuna cewa mutane arba’in 40 ne suka shiga cikin hatsarin 28 sun samu raunuka sai 12 kuma da suka mutu. An kai wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Makarfi domin ci gaba da kula da su,” in ji sanarwar.

Ta ci gaba da cewa, “An sanar da mamallakin motar da ke garin Azare, Bauchi da ya kai rahoto ga rundunar ‘yan sandan Kaduna yayin da direban tirela na cikin wadanda suka rasu”

“Abin da muka shaida a yau abu ne mai yuwuwa don haka ƙudurinmu na ci gaba da tuntuɓar masu ruwa da tsaki musamman ƙungiyoyin sufuri don yin wa’azi tare da wayar da kan direbobinsu game da haɗarin wuce gona da iri tuki mai haɗari da amfani da waya yayin tuki da sauransu.

Karin labari: Daurawa ya sauka daga shugabancin hukumar Hisbah a Kano

“Rundunar ‘yan sanda a Kaduna za ta yi kokarin ci gaba da yin aiki tukuru tare da hada kai da masu ruwa da tsaki a harkar sufuri da kuma kafafen yada labarai wajen yin fadakarwa.

Sanarwar ta rawaito Kwamandan FRSC na Kaduna, Kabir Y Nadabo yana cewa, ”Ina so in yi kira ga masu ababen hawa da su saba da al’ada da kuma tafiyar da tuki cikin aminci musamman a manyan tituna.

Ina fatan zan yi amfani da wannan kafar domin in yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa irin goyon bayan da Hukumar FRSC ke yi a Jihar, da kuma yadda kafafen yada labarai suka yi daidai da kimar FRSC wajen jaddada bayanan lafiya.’’

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here