
Hukumar kai ɗaukin gaggawa ta Najeriya Nema, ta ce za ta tsaurara tsaro a rumbunan ajiye kayan abincinta da kuma ofisoshinta da ke faɗin Najeriya domin kare su daga ɓata gari.
Hakan na zuwa ne bayan harin da aka kai kan wani daga cikin rumbunanta da ke Abuja, babban birnin tarayya a ranar Lahadi.
Wasu matasa ne ake zargin sun kai farmaki kan rumbun wanda ke unguwar Gwagwa da ke Abuja, inda suka yi awon gaba da kayan abinci da kuma sauran abubuwan da aka ajiye a rumbun.
Karin labari: Sarkin Kano ya bukaci ‘yan kasuwa su rage farashin kayan abinci
Wata sanarwa da ta samu sa hannun mai magana da yawun hukumar ta NEMA, ta ce “Shugaban hukumar na ƙasa, Mustapha Ahmed ya bayar da umarnin a tsaurara tsaro a ofososhi da kuma rumbunan ajiye kayan hukumar a faɗin Najeriya domin kaucewa kutsawa cikin su.”
Najeriya dai na fama da matsi na tattalin arziƙi, inda mutane da dama ke kokawa kan rashin abinci da tsadar kayan masarufi.
Kafin fasa rumbun ajiye abincin a Abuja, an samu rahotannin yadda mutane suka farwa motocin dakon kayan abinci tare da yin wawason abin da suke ɗauke da shi a wasu sassan ƙasar.
Karin labari: “Na dauki laifin tsanani da tsadar rayuwa da ‘yan kasa ke ciki” – Tinubu
Ko a makon da ya gabata kungiyar ƙwadago ta NLC ta gudanar da wata zanga-zangar yini ɗaya domin matsawa gwamnati lamba kan ta ɗauki matakan da suka dace wajen kawo sauƙi ga matsalar rayuwa da al’umma ke ciki.
Gwamnatin dai ta ce ta fito da tsarin raba kayan tallafi ga al’umma da kuma baiwa masu ƙaramin ƙarfi tallafin kuɗaɗe.











































