
Shugaba Bola Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri su kuma ci gaba da juriya dangane da halin matsi da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya ba da tabbacin cewa akwai haske nan gaba kadan.
Shugaban ya ce yana da cikakkiyar masaniya kuma ya dauki alhakin matsalolin da ‘yan Najeriya ke fuskanta saboda manufofin gwamnati.
Karin labari: Da Dumi-Dumi: Gwamnatin Kano ta dakatar da nadin Hakimi a Bichi
Ya ce ba zai yi korafi ba amma yana maraba da duk sukar da ake yi masa tunda shi ne ya nemi zama shugaban Najeriya.
Shugaban ya yi wannan jawabi ne a Akure, babban birnin jihar Ondo, a ziyarar da ya kaiwa shugaban kungiyar kabilar Yarbawa ta Afenifere a ranar Laraba.











































