Yanzu-yanzu: Majalisar Dattawa ta fara zaman gaggawa kan gyaran Dokar Zaɓe

Senate 1 750x430

A ranar Talata, Majalisar Dattawan Najeriya ta fara wani zama na gaggawa domin tattauna batun gyare-gyaren Dokar Zaɓe da ke jawo ce-ce-ku-ce, a daidai lokacin da aka fara zanga-zanga a harabar Majalisar sakamakon cire sashe da ke wajabta aika sakamakon zaɓe ta hanyar na’urar lantarki kai tsaye.

Wannan zama na musamman ya zo ne ƙasa da mako guda bayan amincewa da Kudirin Gyaran Dokar Zaɓe na 2026, tare da ƙaruwar matsin lamba daga ƙungiyoyin farar hula, jam’iyyun adawa, ƙungiyoyin kwadago, ƙungiyoyin ƙwararru, shugabannin yankuna da ƙungiyoyin matasa, waɗanda ke zargin ’yan majalisar da rage sahihanci da amincewar zaɓukan nan gaba.

Masu zanga-zangar, da dama daga cikinsu sun hallara a harabar Majalisar tun da sassafe, suna riƙe alluna masu ɗauke da saƙonni tare da rera taken kira da ke neman a dawo da tsarin aika sakamakon zaɓe ta lantarki da kuma ƙarin gaskiya a tsarin dokoki.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ke jagorantar zaman, wanda sauran sanatoci suka halarta bayan sauye-sauyen da aka samu kwanan nan a tsarin Majalisar Dattawan.

An fara zaman ne da ƙarfe goma sha biyu na rana, inda ake sa ran batun gyaran Dokar Zaɓe zai mamaye tattaunawa, yayin da zanga-zangar ke ci gaba a wajen harabar majalisar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here