Tsohon shugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya bayyana cewa murabus ɗinsa daga mukamin shugaban hukumar ya samo asali ne daga dalilai na ƙashin kansa.
Ya ce murabus ɗin ya fara aiki ne daga ranar Litinin, inda ya jaddada cewa ya yanke shawarar ne bisa lamiri da girmama nauyin da ke tattare da hidimar jama’a.
Jaridar Solacebase ta rawaito cewa Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da ya rattaba wa hannu da kansa, wadda aka fitar a birnin Abuja.
A cewarsa, shawarar barin mukamin ta biyo bayan dogon tunani da kuma yin shawara da iyalansa, ba tare da wani matsin lamba ba.
Ya bayyana cewa murabus ɗinsa ya dace da tanadin sashe na 3(6) na dokar kafa hukumar aikin hajji ta ƙasa ta shekarar 2006, inda ya mika rubutacciyar takardar murabus ga Shugaban ƙasa Bola Tinubu kamar yadda doka ta tanada.
Farfesa Abdullahi Saleh Usman ya nuna godiya ga Shugaban ƙasa Bola Tinubu bisa amincewa da ba shi damar yi wa ƙasa da al’ummar Musulmi hidima ta wannan muhimmin matsayi.
Haka kuma ya yaba wa Mataimakin Shugaban ƙasa Kashim Shettima bisa jagoranci, ƙarfafawa da goyon bayan da ya samu a tsawon lokacin da ya rike mukamin.
Ya kuma miƙa godiya ga mambobin kwamitin gudanarwa, shugabanni da ma’aikatan hukumar, inda ya yaba da haɗin kai, jajircewa da ƙwarewar da suka nuna wajen aiwatar da ayyukan hukumar.
Har ila yau, ya nuna godiya ga hukumomin jin daɗin alhazan jihohi, kamfanonin yawon buɗe ido, ɓangaren jiragen sama da masu samar da ayyuka, da kuma abokan hulɗa a ƙasar Saudiyya, waɗanda haɗin gwiwarsu ya taimaka wajen inganta aikin hajjin Najeriya.
Tsohon shugaban hukumar aikin hajji ta ƙasa ya jaddada cewa murabus ɗinsa bai samo asali daga wata rashin jituwa ko gamsuwa da hukumar, gwamnati ko ayyukan da aka aiwatar ba.
Ya bayyana fatan Allah Ya karɓi ayyukan da aka yi, ya shiryar da Shugaban ƙasa da sabon shugabancin hukumar, tare da yi wa alhazan da za su zo gaba fatan samun hajji karɓaɓɓe.
NAN












































