Atiku da Makinde sun ziyarci IBB a Minna

aB4P Ng4

Tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, ya ziyarci gidan tsohon Shugaban Mulkin Soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), da ke a Minna, Jihar Niger, a ranar Talata.

Atiku ya isa gidan IBB ne jim kaɗan bayan ƙarfe 1 na rana, inda nan take ya shiga wata ganawa a bayan fage tare da tsohon shugaban.

Gwamna Seyi Makinde ya haɗu da shi da misalin ƙarfe 2:10 na rana, bayan haka tattaunawar sirrin ta fara.

Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a bayyana cikakkun bayanai kan abin da aka tattauna ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here