Matatar Mai ta Dangote ta rage farashin fetur da Naira 25 kan kowace lita

Pump price 1

Matatar Mai ta Dangote ta rage farashin fetur da Niea 25 kan kowace lita, inda ta sauke farashin daga Naira 799 zuwa Naira 774 kan kowace lita.

An sanar da masu sayar da mai canjin farashin a daren jiya, tare da tabbatar da cewa sabon farashin ya fara aiki nan take a faɗin ƙasa.

Sanarwar da matatar ta fitar ta ce wannan sauyi zai ƙara ƙarfafa gogayya ga kayayyakin da aka tace a cikin gida, ganin cewa farashin fetur da ake shigowa da shi daga Lome a halin yanzu na kusan Naira 793 kan kowace lita, idan aka kwatanta da farashin na matatar Dangote na Naira 774 kan kowace lita.

Ragin farashin da aka yi a ranar Talata shi ne na baya-bayan nan a jerin sauye-sauyen farashin wannan muhimmin kayayyaki, wanda masu lura da al’amura suka ce yawanci canjin darajar Naira da farashin danyen mai a kasuwar duniya ne ke jawo shi, da sauran dalilai.

A bara, farashin fetur na kayayyakin ya rika zagayawa tsakanin Naira 700 zuwa sama da Naira 800 kan kowace lita, lamarin da ya shafi farashin sayarwa ga masu amfani.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here