Yajin aiki: Ma’aikatan shari’a sun kulle alkalai da lauyoyi da masu kara

Strike JUSUN 750x430

A yau Litinin ne ma’aikatan wata babbar kotun tarayya ta kasa reshen kungiyar ma’aikatan shari’a ta Najeriya JUSUN, suka kulle alkalai da lauyoyi da sauran ma’aikata har ma da masu kara tare da hana wasu mutanen shiga kotun biyo bayan yajin aikin da kungiyar ta ke yi.

Binciken da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ya yi a shalkwatar babbar kotun tarayyar da ke kan titin Shehu Shagari a Abuja ya nuna cewa duk kofofin shigar ta na kulle.

An hana alkalai da ma’aikata da lauyoyi da kua masu kara da sauran jama’a damar shiga yayin da harkokin yau da kumma da na kasuwanci a cikin kotun da kewayenta suka tsaya cak.

IMG 20250602 092432 768x576 1

Haka kuma, NAN ta ruwaito cewa kungiyar ta JUSUN ta kasa a ranar 30 ga watan jiya na Mayu a wata takardar da mukaddashin sakatarenta na kasa, M.J Akwashiki, ya fitar ta bukaci daukacin shugabannin kungiyoyin da cewa daga tsakar daren Lahadi, 1 ga watan Yuni, ta umurci dukkan mambobinsu da su zauna a gida.

Ya ce, “Wannan umarnin ya biyo bayan tarukan da ba su da amfani da aka gudanar da Ministan Kwadago da samar da ayyuka da ke sasantawa a kan matsalolin da ma’aikatan ke fuskanta.
Kokarin tattaunawa da wasu daga cikin shugabannin kungiyar ya ci tura domin an ce suna cikin wani taro.

Ko da yake an samu rahotannin cewa wasu sassan kungiyar sun janye daga yajin aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here