Jagoran jam’iyyar APC na kasa, Sanata Bola Tinubu, ya ce a shirye yake ya yiwa Najeriya hidima tare da yin aiki kishin kasa domin inganta kasar.
Tinubu, ya bayyana haka a wata ziyarar da ya kai wa Ataoja na Osogbo, Oba Jimoh Olanipekun, a fadarsa, a ranar Juma’a, ya ce yana da ingancin da Najeriya ke nema a matsayin shugaban da zai bunkasa kasar.
A cewar sa, “Ba zan bari ‘yan Najeriya su yi kasa a gwiwa ba. Ina da kwakwalwa da iya aiki. Ko kun taba ji sun ce ba zan iya ba?’ Ina da lafiya. Kawai Na gyara gwiwa ta kawai.’’
Tsohon gwamnan jihar Legas ya bayyana cewa kasar nan tana da girma, wadata, hadin kai, ba a Afirka kadai ba har ma a duniya.
Ya ce: “Na baiwa kaina damar zama shugaban Tarayyar Najeriya. Na sanar da Buhari haka. Na ce masa ina so in yi wa kasata hidima gwargwadon iyawata.
“Allah ya albarkace mu da dukkan albarkatu – na mutum da na duniya. Abinda kawai ake bukata shine amfani da albarkatun domin samun ci gaba.”
Da yake maida jawabi Oba Olanipekun ya yi addu’ar Allah ya sa burin Tinubu ya kai ga nasara, yana mai cewa Tunubu yana duk wani abu da ake bukata don ciyar da kasa gaba.












































