A yammacin ranar Talata ne fadar shugaban kasar Najeriya ta bayyana cewa, shugaba Bola Tinubu ya damu da hauhawar farashin kayayyakin abinci a kasar nan biyo bayan zanga-zangar da ta gudana a jihohin Kano da Neja.
Ta kuma umarci kwamitin shugaban kasa kan bada agajin gaggawa da ta dauki matakin gaggawa domin duba lamarin.
Malam Mohammed Idris ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa ne ya bayyana hakan bayan taron kwamitin a ranar Talata a babban birnin tarayyar Abuja.
Karanta wannan: Super Eagle: ‘Yan Afirka ta Kudu na barazanar kaiwa ‘yan Najeriya hari
Wasu masu zanga-zangar sun tare wata babbar hanya a jihar Neja ranar litinin domin nuna rashin amincewa da karin farashin kayan abinci da ake ci gaba da yi.
Haka kuma wasu mata a Kano a makon da ya gabata sun yi zanga-zangar nuna rashin amincewa da karin farashin fulawa a jihar Kano.
Alkaluman baya-bayan nan da Hukumar Kididdiga ta Kasa NBS ta fitar, ya nuna hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya da kusan kashi 30 cikin 100, wanda akasari ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci a fadin kasar.
Karanta wannan: Jihar Anambra: ‘Yan Sanda na neman jami’inta bisa zargin kisan kai
Bayan ganawa da ‘yan kasuwar Kano a ranar Litinin, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin sanar da shugaban kasar cewa ‘yan Najeriya na cikin wahala.
Idris ya shaidawa manema labarai a yammacin ranar Talata cewa, shugaba Tinubu ya damu da yadda ake samun sauki da kuma yadda ake samun kayan abinci a fadin kasar nan.
“Gwamnati ta damu matuka da halin da ‘yan Najeriya ke ciki, musamman abin da ya faru a Minna.
“Saboda haka gwamnati na daukar wasu matakai don tabbatar da cewa ‘yan Najeriya sun samu sauki dangane da samar da abinci.”
Karanta wannan: ‘Yan ƙasa da shekaru 18 kawai za’a bawa takardar Haihuwa – NPC
Idris ya ce za’a cigaba da taron kwamitin har zuwa ranar Alhamis, inda ya kara da cewa tuni aka fara daukar wasu muhimman matakai da za su daidaita wannan mummunan lamari.
Ya ce gwamnati na sane da yadda wasu ke haifar da karancin abinci saboda tsadar sa da kuma faduwar darajar Naira.
Taron ya samu halartar shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Femi Gbajabiamila da gwamnan babban bankin kasa Yemi Cardoso da ministan kudi Wale Edun da kuma mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu.
Sauran sun hada da Ministan Noma Sanata Abubakar Kyari da na Kasafin Kudi da Tsare Tattalin Arziki Bagudu Atiku da sauran masu ruwa da tsaki a zaman kamar yadda NAN ta rawaito.