Super Eagle: ‘Yan Afirka ta Kudu na barazanar kaiwa ‘yan Najeriya hari

Super Eagle, Afrika ta kudu, barazanar, hari, 'yan najeriya
Gwamnatin Kasar nan ta roki ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu da su kaucewa bayyana farin cikin su a fili idan kungiyar Super Eagles ta samu nasara a kan...

Gwamnatin Kasar nan ta roki ‘yan Najeriya mazauna Afirka ta Kudu da su kaucewa bayyana farin cikin su a fili idan kungiyar Super Eagles ta samu nasara a kan Bafana-Bafana a gasar cikin kofin Afirka dake gudana a Abidjan.

Gobe ne ake saran kasashen biyu su fafata domin samun tikitin zuwa wasan karshe na gasar dake ci gaba da dauke hankalin masu sha’awar kwallon kafa a kasashen duniya.

‘Yan Najeriya da dama dake zama a biranen Afirka ta Kudu sun bayyana samun sakonnin barazana daga wasu ‘yan kasar dangane da wannan wasa da za’a yi a gobe laraba.

Karanta wannan: Jihar Anambra: ‘Yan Sanda na neman jami’inta bisa zargin kisan kai

Daya daga cikin shugabannin ‘yan Najeriyar mazauna kasar, Godwin Okeke yace ba’a yau suka fara fuskantar irin wannan barazana daga mutanen kasar ba, inda yace ko a shekarun baya da kungiyar kwallon kafa ta mata ta je can domin karawa da takwarorinsu na Afirka ta kudu, su da magoya bayan su da kyar suka sha, sakamakon hare haren da aka kai musu da duwatsu saboda nasarar Najeriyar.

Sanarwar da ofishin jakadancin Najeriya dake Pretoria ya gabatar, ya bukaci ‘yan Najeriya suyi taka tsan-tsan wajen kalaman su da kuma inda suke shiga domin kaucewa barazanar da wasu bata gari ke yi na kai musu hari.

Karanta wannan: ‘Yan ƙasa da shekaru 18 kawai za’a bawa takardar Haihuwa – NPC

Ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da su kaucewa bukukuwa idan kasar ta samu nasara, tare da kuma kira a gare su da su zama masu bin doka da oda a koda yaushe.

‘Yan kasar Afirka ta Kudu sun dade suna kai munanan hare-hare a kan ‘yan Najeriya da kuma wasu ‘yan Afirka saboda zargin da suke musu na mamaye harkokin kasuwanci da ayyukan yi, yayin da suke zargin bakin da kuma hada-hadar kwaya.

A shekarar 2019 a kalla baki 10 aka kashe a Afirka ta Kudu lokacin da wasu bata garin matasa suka dinga kai hari a kan ‘yan kasashen Afirka da kuma wuraren kasuwancinsu, abinda ya tinzira tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari janye jakadan kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here