
Rundunar ‘yan sandan jihar Anambra ta sanar da kama jami’inta, Insfekta Audu Omadefu mai lamba (AP No.362178) da laifin kisan kai.
DSP Tochukwu Ikenga jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Awka ranar Talata.
Karanta wannan: ‘Yan ƙasa da shekaru 18 kawai za’a bawa takardar Haihuwa – NPC
Ikenga ya ce rundunar ta bukaci daukacin al’umma da suka ga wanda ya gudu ko kuma suka samu labarin inda yake, a hanzarta kai rahoto ofishin ‘yan sanda mafi kusa.
Ya ce jama’a na iya kiran lambar su kai tsaye a 07039194332 ko kuma PPRO na hukumar akan 08039334002.
Rundunar ‘yan sandan ta tabbatar wa jama’a cewa duk wani bayani da aka bayar a kan haka za’a yi amfani da shi cikin gaggawa a sirrince kamar yadda NAN ta rawaito.