Sai da Buhari ya amince sannan na bar APC zuwa SDP – El-Rufai

el rufai Speaking

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce bai bar jam’iyya mai mulki ta APC ba har sai da tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya amince da batun barinsa jam’iyyar APC da komawa jam’iyyar SDP.

“Da saninsa na bar APC. Sai da na je ranar Juma’a na faɗa masa cewa zan bar jam’iyyar. Saboda babu wani abun da nake yi ba tare da na sanar da shi ba.

Ko lokacin da nake gwamnan Kaduna da zan naɗa kwamishoni sai da na kai masa jerin sunayen domin ya duba ya gani ko a ciki akwai wanda ya taɓa zagin sa.

Labari mai alaƙa: El-Rufai ya fice daga jam’iyyar APC, ya koma SDP

Bayan ya duba ya ce ba matsala Allah ya yi albarka. Duk abin da zan yi sai na yi shawara da shi.” In ji Malam El-Rufai.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here