Obasanjo ya bayyana aikin titin Legas zuwa Calabar a matsayin almubazzaranci da rashawa

Olusegun Obasanjo new 750x430

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya bayyana aikin titin Legas zuwa Calabar a matsayin aikin almubazzaranci da rashawa.

Hakazalika ya caccaki gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu kan kashe naira biliyan 21 wajen gina sabon gidan mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, inda ya bayyana hakan a matsayin don zuciya da kuma samar da wata mafaka domin satar dukiyar al’umma.

Tsohon shugaban ya bayyana hakan ne a babi na shida na sabon littafinsa mai suna ‘Nigeria: Past and Future,’ inda ya zana hotuna da halayen manyan shuwagabannin hukumomin tarayya da na jihohi.

Littafin na daya daga cikin sabbin litattafai biyu da aka kaddamar domin murnar cikar Obasanjo shekaru 88 a makon jiya.

Karin karatu: Na yi nadamar rushe zaɓen June 12 – IBB
Ministan ayyuka, David Umahi, ya bayyana cewa babbar hanyar Legas zuwa Calabar mai tsawon kilomita 700 za ta ci Naira biliyan 4.93 a kowace kilomita, inda ya bayyana cewa an bayar da kwangilar ne bisa ka’ida ta kudi ba wai hadin gwiwar jama’a da masu zaman kansu ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here