NASU da SSANU sun bai wa Gwamnatin tarayya wa’adin kwana 7 kafin su fara yajin aiki

SSANU NASU

Kwamitin hadin gwiwa na ƙungiyar ma’aikatan da ba na ilimi ba (NASU) da manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya (SSANU) sun ba gwamnatin tarayya sanarwar fara yajin aiki nan da kwanaki bakwai.

Kungiyoyin sun aika da wasikar ne ga Ministan Kwadago da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi, inda suka bayyana cewa idan gwamnati ta kasa warware matsalolin da suka dade suna korafi a kai cikin wa’adin, za su shiga yajin aiki.

Wasikar wacce ta samu sa hannun Babban Sakataren NASU, Prince Peter Adeyemi, da Shugaban SSANU, Mohammed Ibrahim, an rabawa manema labarai a Abuja ranar Litinin.

Cikin korafe-korafen da suka gabatar akwai rabon naira biliyan 50 na hakkokin ma’aikata, albashin da aka rike, bashin karin kashi 25/35 cikin 100 na albashi da ba a biya ba, da kuma jinkirin kulla sabuwar yarjejeniyar 2009 tsakanin gwamnati da kungiyoyin.

Kungiyoyin sun zargi gwamnati da nuna wariya, inda suka ce ma’aikata a cibiyoyin jami’o’i na hadin gwiwa an ware su gaba daya daga rabon kudin naira biliyan 50, yayin da sauran mambobi suka samu kadan fiye da abin da ya dace.

Haka kuma sun bukaci a biya musu dukkan bashin albashin da aka rike da kuma karin albashin da gwamnati ta dade tana bayar da alkawari ba tare da cikawa ba. Sun ce duk da tabbacin da gwamnati ta sha bayarwa, ba a yi wani muhimmin mataki ba.

Haka zalika, NASU da SSANU sun yi zargin cewa gwamnati ta yi watsi da kungiyoyin da ba na koyarwa ba a tattaunawar sake fasalin yarjejeniyar 2009, lamarin da suka bayyana a matsayin rashin adalci.

A cewar kungiyoyin, daga ranar 15 ga Satumba, 2025 ne wa’adin kwanaki bakwai ya fara aiki, kuma idan gwamnati ta yi biris, za su dauki matakan yajin aiki na gaba daya.

NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here