Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Jigawa, Haruna Aliyu Dangyatin, ya tsira daga wani mummunan hadarin mota da ya rutsa da tawagar rakiyarsa yayin da yake hanyarsa zuwa karamar hukumar Maigatari.
Rahotanni sun bayyana cewa Kakakin yana kan tafiya ne domin halartar taron siyasa na gwamnati da ake kira “Gwamnati da Jama’a” lokacin da lamarin ya faru.
Motar Toyota Hilux mai bude wacce ke dauke da jami’an ‘yan sanda masu gadinsa, ta kubuce wa direba sannan ta kife, inda hakan ya jefa jami’an cikin hatsari.
Shaidu sun bayyana cewa sauran motocin da ke cikin rakiyar, ciki har da wadda shugaban yake ciki, sun yi nasarar kaucewa kuma suka tsaya daga dan nesa wajen da hatsarin ya auku.
An bayyana cewa jami’an ‘yan sandan da suka jikkata an garzaya da su Asibitin Gumel cikin a sume, amma daga bisani sun farfado sai dai motar ce ta lalace sosai.
Mataimakin shugaban Majalisar, Aqeel Akilu, ya tabbatar da faruwar hadarin, inda ya bayyana cewa babu wanda ya rasa ransa, kuma dukkan jami’an da suka jikkata yanzu suna samun sauki bayan an sallame su daga asibiti.
NAN













































