DSS ta kai Sowore, kamfanin X da Meta kotu

DSS with Sowore 750x430 (1)

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta shigar da ƙarar laifi a gaban Babbar Kotun tarayya da ke Abuja kan ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore.

A cikin ƙarar, DSS ta haɗa da kamfanin X, mallakar shafin sada zumunta na X, da kuma kamfanin Meta mallakar kamfanin Facebook, a matsayin masu ƙara na biyu da na uku.

Bisa ga takardun kotu da aka shigar ranar 16 ga Satumba, 2025, DSS ta zargi Sowore da bata sunan shugaban ƙasa Bola Tinubu, inda ta yi ikirarin cewa ya kira shugaban ƙasa “ɓarawo” ta shafukan sada zumunta na X da Facebook, yayin ziyarar aiki da Tinubu ya kai ƙasar Brazil a watan Agusta.

Takardar ƙarar wacce M.B. Abubakar, Daraktan Gabatar da Ƙarar Lauya a ma’aikatar shari’a ta tarayya ya shigar tare da wasu lauyoyi, ta ƙunshi tuhuma guda biyar kan Sowore.

Haka kuma DSS ta gabatar da hujjoji ciki har da kwafi na rubutun Sowore a X da Facebook, da wasiku da aka rubuta wa X da Meta.

A halin yanzu dai, har yau ba a bai wa wata kotu wannan shari’a ba, kuma babu ranar da aka tsayar don gurfanar da Sowore.

Wannan lamari ya ƙara haɓaka takaddama tsakanin ɗan gwagwarmayar da hukumar tsaron cikin gida ta ƙasar.

A baya, DSS ta buƙaci Sowore ya janye kalaman nasa tare da bada haƙuri a manyan jaridun ƙasa da kuma shafukan sada zumunta, amma ya ƙi amincewa, yana mai cewa maganganunsa ƙarƙashin kariyar ’yancin faɗar albarkacin baki suke.

Wannan rashin janye magana ce ta sa DSS ta sha alwashin bin matakin shari’a, lamarin da ya janyo shigar da ƙarar yanzu.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here