Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya rantsar da sabbin kwamishinoni bakwai da ya nada tare da raba musu ma’aikatu.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya raba musu ma’aikatun ne yau Litinin yayin bikin rantsar da su da aka gudanar a fadar gwamnati.
SolaceBase ta ruwaito cewa Shehu Wada Shagagi an tura shi ma’aikatar Zuba Jari da harkokin Kasuwanci da Masana’antu sai Dakta Dahiru Muhammad Hasim ma’aikatar Muhalli, Ismail Aliyu ma’aikatar Kudi sai Gaddafi Shehu ma’aikatar kula da harkokin makamashin lantarki da kuma Abdulkadir Abdulsalam da gwamnan ya tura shi ma’aikatar raya karkara da birane da kuma Ibrahim Waiya ma’aikatar yada labarai da kuma Nura Iro Maaji ma’aikatar kula da ƙadarorin gwamnati.
Gwamnan, ya bukaci wadanda aka nada da kada su ci amanar amanar da gwamnatinsa ta damka musu don ciyar da Kano gaba.