Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu, ya bukaci yar gwagwarmayar nan ta Arewa Hajiya Naja’atu Muhammad da ta nemi afuwarsa kan wasu kalamai da ta yi a cikin wani faifan bidiyo da aka wallafa a TikTok, ko kuma ya maka ta a gaban kotu.
A cikini bidiyon ta zarge shu da munafunci sakamakon yin aiki da shugaban kasa Bola Tinubu da wasu da ya zarga da kasancewa cikin wadanda suka fi cin hanci a Najeriya lokacin yana shugaban hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC. .
Haka kuma Ribado ya nemi jama’a da su watsi da kalaman nata kasancewar faifan bidiyon na ci gaba da yaduwa.
Shugaba Tinubu Ya Nada Ribadu, Alake da Wasu 6 a Matsayin Mashawarta
Ribado a wata wasika ta hannun lauyansa, Dokta Ahmed Raji, SAN, zuwa ga Naja’atu Muhammad, ya ce a kowane lokaci bai taba rike irin wannan ra’ayi ba game da Tinubu da wasu da Najatu Muhammad ta ambata a cikin bidiyon ta.
A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 4 ga Fabrairu, 2025, mai dauke da sa hannun Dr. Raji, Ribadu ya ce manufar Najatu Muhammad a cikin faifan bidiyon ita ce ta kawo masa sabani da abin kunya.
Ya kuma nemi ta fito manyan jaridun kasar nan 5 ta nemi afuwarsa, idan ta gaza janye kalaman ta cikin kwanaki bakwai to kuwa zai nemi hakkin sa a gaban Kotu.













































