Ƴan bindiga sun kai hari shingen binciken sojoji a kusa da Abuja

Abuja city
Abuja city

Wasu da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne sun kai hari wani shingen bincike na sojoji da ke kusa da dutsen Zuma da ke kusa da babban birnin Abuja.

Ganau sun shaida wa BBC Hausa cewa maharan sun je wurin ne bayan magariba inda suka ɓude wuta a shingen binciken.

Jama’ar da ke wurin sun ce sun ji ƙarar harbin bindiga ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa wadanda ke kusa da wurin suk gudu domin neman mafaka.

Rahotanni dai sun ce maharan sun yi musayar wuta da jami’an tsaro, sai dai babu tabbaci kan ko akwai wanda ya jikkata ko ya rasa ransa. Ko da yake wasu rahotanni daga kafafen watsa labaran kasar na cewa an kashe sojoji da dama.

Wani ganau ya bayyana wa BBC cewa suna cikin mota suna tafiya sun je daidai wurin dutsen Zuma, sai suka ji ƙarar bindiga ba ƙaƙƙautawa, lamarin da ya sa suka bar motocinsu suka arce cikin daji.

“Mun bar motocinmu a buɗe muka shiga daji a guje, muka je can kusa da Madallah u-turn, dama mun taho ne daga Abuja za mu je Suleja, can dai bayan kamar minti 15 zuwa talatin haka sai muka yi sa’a mutane suna ta juyawa mu ma muka je muka ɗauko motarmu muka juyo,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ko a lokacin da suka bar wurin, ƴan bindigar na ci gaba da buɗe wuta ba ƙaƙƙautawa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here