Da ɗumi-ɗumi: Kotu ta ba da belin Muhuyi Magaji Rimingado

IMG 20220429 120318 866 678x381 1
IMG 20220429 120318 866 678x381 1

Wata Kotun Majistare da ke Kano, ta bayar da belin dakataccen shugaban hukumar karɓar ƙorafi da yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar, Muhuyi Magaji Rimingado.

A yau Juma’a ne ƴan sanda suka gurfanar da Muhuyi Magaji Rimingado a gaban kotu bisa bisa zargin bayar da bayanan ƙarya.

Solacebase ta ruwaito cewa babban alkalin kotun, Aminu Gabari, ya bayar da belin wanda ake ƙaran akan kuɗi naira dubu ɗari biyar tare da mutane biyu da za su tsaya masa wadanda suka haɗa ɗan uwa ko uba a wajensa da kuma babban limamin masallacin Juma’a na Sharada ko Ja’en.

Alƙalin, ya kuma umarci wanda ake ƙara da ya miƙa takardun tafiye-tafiyensa ga kotun.

An kama dakataccen shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ne a Abuja ranar Alhamis, jim kaɗan bayan an tantance shi a matsayin dan takarar gwamnan Kano a ƙarƙashin jam’iyyar PDP

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here