Kano ta kaddamar da kwamitin gudanarwa don yaki da rashawa da tabbatar da gaskiya

Governor Abba Kabir Yusuf 640x430 (2)

Shugabar Ma’aikata ta Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Maimota, ta kaddamar da wani babban Kwamitin Gudanarwa don tabbatar da aiwatar da Tsarin Yaki da Rashawa na Jihar Kano (KANSACS) ta hanyar Shirin Kyautata Ayyuka da Gaskiya na Ma’aikatan Gwamnati (SSDTI).

A cewar wata sanarwa da Abdulkarim Ibrahim I. DPRS/Ag. DPE na Ofishin Shugabar Ma’aikata ya fitar, ya bayyana cewa an kaddamar da kwamitin ne a dakin taro na ofishin.

Wannan shiri ya tattara manyan hukumomin gwamnati waje guda domin karfafa gaskiya, rikon amana, da kuma inganta ayyuka a daukacin ma’aikatun gwamnatin jihar.

Yayin kaddamar da kwamitin, Maimota ta bayyana cewa shirin SSDTI wani muhimmin bangare ne na kudirin gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na ganin ma’aikatan jihar sun dace da bukatun karni na 21.

Ta umarci mambobin kwamitin da su kasance masu sanya idanu da kuma inganta ayyuka ta hanyar bunkasa tafi da ayyuka cikin gaskiya, hanzarta gudanar da ayyukan gwamnati, soke duk wata dabi’ar jinkiri ta gudanarwa da ke kawo cikas ga shugabanci nagari.

Haka kuma, Shugabar Ma’aikatan ta jaddada rawar da Hukumar Karbar Korafe-korafe da Yaki da Rashawa ta Jihar Kano (PCACC) za ta taka, tana mai cewa sanya hukumar a ciki yana nuna manufar gwamnati na bas ani ba sabo ga rashawa.

Ta bayyana cewa za a auna nasarar kwamitin ne ta hanyar sauye-sauyen da aka aiwatar a aikace, ba wai yawan shawarwarin da aka rubuta ba.

Tun da fari, Shugaban Kwamitin Gudanarwar kuma Shugaban PCACC, Sa’idu Yahaya, ya bukaci mambobin kwamitin da su yi nazari a kan Tsarin Aiki na KANSACS na shekarar 2024–2028 domin canza manufofinsa su koma sauye-sauye na zahiri a ma’aikatunsu.

Yahaya ya yi gargadin kada a bari tsarin ya zama kawai takarda ce ta manufofi ba tare da aiwatarwa ba, inda ya bayyana shi a matsayin cikakken tsarin rage rashawa da karfafa rikon amana a Jihar Kano.

Kwamitin ya kunshi wakilai daga manyan hukumomin gwamnati, ciki har da Hon. Abubakar Dalladi Isa Shugaban Kwamitin Majalisa a kan Ayyukan Ma’aikata, Salisu Mustapha Babban Sakatare, SSG Sabi’u Shu’aibu Muhammad Babban Sakatare, Ma’aikatan Gwamnati da Kyautata Ayyuka.

Sauran sun hada da Ahmad M. Tahir Lauyan Gwamnati/Babban Sakatare, Ma’aikatar Shari’a, Amina Yusuf ‘Yargaya – Babban Sakatare, Ma’aikatar Kudi, Umma Dallatu Babban Sakatare, Ma’aikatar Tsare-tsare da Kasafin Kudi, Fatima Adamu Babban Sakatare, Ma’aikatar Kananan Hukumomi.

Sai kuma Pharm. Aminu Bashir Sabon Babban Sakatare, Ma’aikatar Ilimi, Abdulkadir Shehu Sabon Babban Sakatare, Ma’aikatar Lafiya, Hannatu Ado Gwaram Babban Sakatare, SERVICOM da kuma Engr. Abdulrazak Haruna Babban Sakatare, Ma’aikatar Siyan Kayan Gwamnati da Sanya Idanu kan Ayyuka.

Shugaban Sakatariyar KANSACS, Isah Mansur Bello, shi ne zai kasance sakataren kwamitin domin daidaita ayyukan sakatariyar, bayar da rahotanni da kuma duba ci gaban da aka samu.

Wannan shiri ana sa ran zai karfafa rikon amana na hukumomi, inganta ayyukan gwamnati, da kuma rage rashawa da matsalolin gudanarwa a fadin Jihar Kano.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here