Wike ya dakatar da Daraktan FCTA kan bayar da amincewa ba kan ka’ida ba a Green Areas

Wike NBA 750x430

Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya bayyana cewa an dakatar da wani darakta a karkashin Hukumar Gudanarwar Babban Birnin Tarayya (FCTA) a karkashin ka’idojin aikin gwamnati, bayar da izinin wicin-gadi ga ‘yan kasuwa a wuraren da aka ware don dashen itatuwa (green zones).

A cewarsa, gwamnatinsa ta tsananta sanya idanu da daukar matakai kan keta dokoki da ke da alaka da ambaliyar ruwa da aka yi kwanan nan a hanyar Airport da kuma gundumar Lokogoma.

Yayin da yake jawabi ga manema labarai ranar Laraba a Port Harcourt, babban birnin jihar Rivers, Wike ya bayyana cewa bayan rugujewar gine-ginen da aka yi ba bisa ka’ida ba, FCTA tana kuma daukar tsauraran matakai na tsawon hukunci ga jami’an gwamnati da ke taimakawa wajen mamaye Green zones da hanyoyin ruwa ba bisa doka ba.

Ya kuma bayyana cewa wani jami’in daban ya fuskanci horo saboda rabon filayen shakatawa ba bisa ka’ida ba da sunan yin binciken tsaro.

Wannan bayani ya zo ne daidai lokacin da ministan ya tabbatar da cewa an tura wani babban kwamiti na musamman karkashin jagorancin Babban Sakataren Hukumar Bunkasa na Babban Birnin Tarayya (FCDA) da Daraktan Kula da Ci gaban Gine-gine domin gudanar da binciken gani da ido a yankunan da ambaliyar ta shafa, ciki har da Lugbe da Lokogoma.

“Lokacin da na ji labarin faruwar lamarin, Babban Sakataren FCDA da Daraktan Kula da Gine-gine sun je wurin, ba kawai a hanyar filin jirgin sama ba har ma a Lokogoma, mutum ne ya haddasa shi, za mu iya magance matsalar, babu abin da za mu iya yi ya zama annoba ta daga Allah. Saboda haka, abu ne da ya kamata mu bincika,” in ji shi.

Yayin da yake amincewa da cewa mamakon ruwan saman da aka yi kwanan nan a babban birnin kasar ya kai matakin da ba a taba gani ba, Wike ya jaddada cewa binciken farko ya nuna akwai tsofaffin karya dokokin tsarin birnin Abuja, inda aka gina tsarin gine-gine a kan hanyoyin ruwa na dabi’a da kuma hanyoyin mota da aka ware ba tare da sahihiyar amincewa ba.

Ya lashi takobin cewa gwamnatin za ta dauki duk matakan da suka dace don gyara kura-kuran da aka yi wa tsarin birnin Abuja a daidai hanyar jirgin sama, kuma ba za ta yi jinkirin rushe kowane irin gini da aka samu a kan hanyoyin ruwa ba.

“Daga bincikenmu, yankin Lugbe ya dade yana lalata tsarin birnin Abuja… Cikin shekaru da dama, kana ganin mutane suna gini ba tare da izini ba kuma suna toshe inda ya kamata ya zama hanyar mota. A matsayinmu na gwamnati, ba ma wasa da wannan lamari,” in ji shi.

Game da zargin cewa wasu daga cikin gine-ginen da aka yi wa alama domin rushewa suna da amincewar gwamnatin baya, ya nanata cewa amincewar da aka samu ba bisa ka’ida ba ta hanyar yin amfani da iko ko alfarma ba za ta zama garkuwa ga fuskantar doka ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here