Jami’an ‘yan sanda 5 sun mutu, 11 sun jikkata a wani hadarin mota da ya rutsa da su a Kano

FRSC Accident

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta tabbatar da mutuwar jami’anta biyar sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a garin Karfi da ke karamar hukumar Kura.

Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa hadarin ya kuma yi sanadin jikkata wasu jami’ai 11.

Kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Abdullahi Kiyawa ne ya bayyana faruwar lamarin a ranar Talata, inda ya bayyana cewa jami’an sun yi hatsarin ne a lokacin da suke dawowa Kano daga aiki a hukumance.

“Hatsarin ya afku ne a Karfi mai tazarar kilomita kadan daga Kano, abin takaici jami’ai biyar ne suka rasa rayukansu nan take, yayin da wasu 11 suka samu raunuka daban-daban,” in ji Kiyawa.

A binciken farko da aka gudanar, jami’an na tafiya ne a cikin wata motar bas ta Hummer da ta yi karo da wata tirela da ke faka, lamarin da ya yi sanadin asarar rayuka.

An garzaya da jami’an da suka jikkata zuwa asibitin kwararru na Murtala Mohammed, inda a yanzu haka suke samun kulawa.

Kakakin hukumar FRSC na Kano, Abdullahi Labaran, shi ma ya tabbatar da afkuwar hatsarin, inda ya bayyana cewa ya faru ne sakamakon gudun wuce gona da iri, lamarin da ya sa direban bas din ya rasa iko kafin ya yi karon.

An tura jami’an hukumar zuwa jihar Edo domin gudanar da ayyukan sa ido kan zabe kuma suna komawa Kano a lokacin da hatsarin ya afku.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here