Kungiyar Lauyoyi ta kasa ta bukaci hukumar dake kula da gidan gyaran hali na kasa da kuma hukumar DSS dasu hukunta zami’an su bisa bawa hammata iska da sukai akan Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya.
Kungiyar ta bayyana rigimar da jami’an sukai a matsayin abin kunya da kuma rashin girmama kotu.
Bayanin hakan na dauke a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa baki daya Yakubu Maikyau ya fitar ranar Laraba.
Idon zaku iya tunawa dai jiya aka sami rikici tsakanin jami’an DSS dana NCoS akan wanda zai tafi da Emefiele kafin cika sharadan beli da babbar kotun tarayya dake jihar Legas ta bayar, inda jami’an suka shiga bawa hammata isaka kan tafiya dashi, wadannan suna ni zan tafi dashi, wadannan na ni zan tafi dashi.













































