Jami’ar Bayero da ke Kano (BUK) ta samu lambar yabo ta tagulla biyu a Judo a gasar wasannin jami’o’in Afirka karo na 11 da ke gudana a jihar Legas.
Mujahid Musa dalibi ne a Sashen Accounting, wanda ya yi gasar ajin kilo 73 ne ya samu lambobin yabo.
Nasarar da ya samu ta sa BUK ta kara samun karbuwa a duniya a lokacin gasar.
Da yake mayar magana, Daraktan wasanni na BUK, Farfesa Rabiu Mohammed, ya bayyana jin dadinsa da yadda dan wasan ya taka rawar gani.
Ya alakanta wannan nasarar dalibin da goyon bayan da shugaban jami’ar Farfesa Sagir Adamu Abbas ya ba shi.
Kocin Judo, Ado Cizo, ya bayyana yadda Musa ya dade yana shiga harkar wasan, inda ya ce BUK na da rawar gani sosai a Judo, inda ta samu lambobin yabo da dama a gasa daban-daban a tsawon shekaru.
Mahaifin Mujahid wanda ya halarci gasar, ya bayyana farin cikinsa kan nasarar da dansa ya samu.