An kashe mataimakan Bello Turji yayin da sojoji ke ci gaba da neman shugabanninsu – CDS

Turji Bello 750x430

Babban Hafsan Hafsoshin tsaron kasar nan Janar Christopher Musa, ya ce sojoji sun kashe wasu manyan kwamandoji a sansanin Bello Turji, gawurtaccen dan bindigar daji a jihar Zamfara.

Da yake jawabi a wajen rufe wani taro a Abuja ranar Juma’a, Musa ya bayyana sunayen kwamandojin ‘yan fashin da aka kashe yayin gudanar da aiki da suka haɗar da Kachalla Gwammade da Kachalla Shehu.

Ya ce an kashe ‘yan ta’addan ne a ranar Alhamis da daddare, ya kuma kara da cewa matakin da sojoji suka dauka a Zamfara ya jefa Turji cikin wani yanayi na neman tsira.

Labari mai alaƙa: Fitaccen Dan Ta’adda Bello Turji Na Cikin Tsaka-Mai-Wuya — Rundunar Sojin Najeriya 

“A wani samame da suka kai, sojoji sun kutsa cikin kauyukan Tufan da Mashima, inda suka kara fatattakar kungiyoyin da ke dauke da makamai tare da kara tura su cikin dajin,” in ji CDS.

“Rahotanni sun nuna cewa Turji da Sani Black yanzu haka suna cikin wannan yanki suna neman hanyar tsira yayin da matsin lamba ke karuwa.”

Babban hafsan tsaron ya ce jami’an tsaron sun aike da sako mai karfi ga dukkanin kungiyoyin da ke dauke da makamai a kasar nan cewa, zamanin rashin hukunta su ya kare.

Musa ya kara tabbatar da cewa sojoji za su ci gaba da zage damtse har sai an kawar da dukkan bangarorin ‘yan ta’adda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here