Hukumar Zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sake matsa kaimi wajen kafa kotun hukunta laifukan zabe.
A cewar shugaban hukumar ta INEC, Mahmood Yakubu, matakin ya zama muhimmi saboda koma bayan shari’o’in laifukan zabe da ake fuskanta.
Mahmood ya yi wannan jawabi ne a Abuja ranar Juma’a yayin taron tuntuba na farko da hukumar ta saba yi da manema labarai duk wata uku.
Karin labari: INEC Ta Karawa Jami’ai 1,731 Girma
“Ba a ba da fifiko ga shari’o’in kamar yadda kotuna ke gudanar da shari’o’i iri-iri. Saboda haka, laifukan zaɓe suna gudana daga babban zaɓe zuwa wani wanda wani lokaci yana iya yin tasiri ga ƙaddamar da ƙararrakin. Don haka ya zama wajibi mu sabunta kiran da mu ke yi na a kafa kotun hukunta laifukan zabe da ke da hurumi na musamman da kuma takaitaccen lokaci domin gaggauta gudanar da shari’o’in.”
Shugaban hukumar ta INEC ta yi Allah wadai da jinkirin da ake samu a harkar shari’a, inda ya yi nuni da hukuncin da aka yankewa wani jami’in a Akwa Ibom bayan shekaru shida.
“An yi nasarar gurfanar da wani jami’in lura da zabe a jihar Akwa Ibom a kwanan baya, kuma hakan misali ne, la’akari da yadda hukumar ta ci gaba da bin diddigin lamarin tun daga zaben 2019, aka kwashe kusan shekaru shida ana samun nasarar gurfanar da a gaban kotun shari’a,” inji shi.