Tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai, ya ce ba ya yin riya kuma ba zai iya kasancewa daya daga cikin ‘yan siyasar da suka zama ‘yan wasan kwaikwayo na Nollywood ba ko da sau daya a gwamnati.
A kwanakin baya ne El-Rufai ya shiga musayar yawu da wasu ‘yan gwamnatin shugaba Bola Tinubu.
An fara cece-kuce bayan tsohon gwamnan na Kaduna ya caccaki jam’iyyar APC mai mulki da cewa “Ta baude daga cikin manyan manufofin ta” inda ya ce ya daina amincewa da jam’iyyarsa ta siyasa.
Kalaman El-Rufai ya tayar da kura a fadar shugaban kasa, kuma Daniel Bwala, mai taimaka wa shugaban kasa, ya tambayi El-Rufai ko ra’ayinsa game da APC zai sha bamban idan yana cikin majalisar ministocin Tinubu.
Karanta har ila yau: Badakalar Kudade: Kotu Ta Sake Hana Tsohon Shugaban Ma’aikatan El-Rufai Beli
Da yake mayar da martani kan kalaman Bwala, El-Rufai ya ce har yanzu zai soki APC ko da kuwa yana da hannu a gwamnatin Tinubu.
A Asabar din nan, a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X, tsohon gwamnan Kaduna ya sake yin wasu kalamai na cewa wasu kan zama ‘yan amshin shata da zarar sun samu mukaman siyasa.
Yana mai da martani ne ga wani sakon da wani mai amfani da kafafen sada zumunta, @irahabib ya wallafa.